An kama mataimakin shugaban Facebook a Brazil

'Yan sanda a brazil sun kama mataimakin shugaban shafin Facebook na yankin Latin Amurka.

Sun ce an kama shi ne saboda kamfanin sada zumuntar ya ki bayar da hadin kai wajen yin binciken safarar miyagun kwayoyi.

Hukumomi sun ce Diego Dzodan, dan asalin kasar Ajantina, ya sha kin bin umarnin kotu na mika wasu bayanai daga shafin kamfanin na musayar bayanai na Whatsapp.

Ana tuhumarsa ne a birnin Sao Paulo.

Kamfani Facebook dai ya ce wannan hukunci ya yi tsauri kuma bai dace ba.

A watan Disambar da ya gabata ma wani mai shari'a dan Brazil ya dakatar da kafar sadarwa ta Whatsapp na tsawon sa'o'i 48 bayan da ya ki bin umarnin kotu na musayar bayani a kan wani mugun laifi.

Karin bayani