Iran na son daina cece-kuce da kasashen duniya

Hakkin mallakar hoto ISNA
Image caption Rouhani ya ce 'yan kasarsa sun fi son sassaucin ra'ayi.

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya ce sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar ya nuna cewa kasar ba ta son ci gaba da yin takun-saka tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Mista Rouhani ya yi wannan bayani ne a karon farko tun bayan da ta fito fili cewa jam'iyyarsa ta masu sassaucin ra'ayi ita ce ta lashe akasarin kujerun majalisar dokokin kasar.

Jam'iyyun da ke da tsattsauran ra'ayi sun rasa rinjayen da suke da shi a majalisar dokokin.

Mista Rouhani ya kara da cewa 'yan kasar ta Iran sun nuna wa duniya cewa sun fi amincewa da sassaucin ra'ayi a kan tsattsauran ra'ayi.