'Yan sanda na binciken satar dalibai mata a Lagos

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun matsa kaimi domin ceto matan da aka sace a Lagos.

A Najeriya, rundunar 'yan sanda a jihar Lagos ta baza-komarta a kokarin ceto wasu 'yan mata 'yan makarantar sakandare da wasu mutane dauke da bindigogi suka sace a Ikorodu da ke wajen Birnin Ikkon.

A daren Litinin ne mutanen suka shiga makarantar Sakandare ta Babington Macauly suka sace 'yan matan.

Har yanzu mutanen da ke garkuwa da 'yan matan ba su bayyana dalilin su na yin hakan ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Dolapo Badmus, ya ce har yanzu basu gano mutanen da suka yi garkuwa da matan ba, yana mai cewa suna ci gaba da lalube don gano su.

Garkuwa da 'yan matan na zuwa a lokacin da ake fafatikar neman 'yan matan sakadaren Chibok sama da 200 da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace kusan shekara biyu babu labari.