'Yan gudun hijira na bukatar taimako

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin mutane sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram.

A Jamhuriyar Nijar, 'yan gudun hijirar yankin cencendin Diffa na kokawa da matsalar karancin abinci.

'Yan gudun hijirar sun ce suna samun taimakon abinci ne daga kungiyoyin agaji sai dai ba ya isa, lamarin da ya sa wasu kaura daga sansaninsu.

Wasu daga cikin su da wakiliyar mu a Maradi Tchima Illa Issoufou ta tattauna da su a Maradi, sun shaida ma ta cewa babbar matsalar da suke fuskanta ita ce batun abinci, da ruwan sha mai tsafta da sauran su.

Don haka sun yi kira ga hukumomin agaji da su kai musu dauki, kan halin da su ke ciki.