Biritaniya na neman dan kasarta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai Ministan Biritaniya, David Cameron

Ofishin jakadancin Biritaniya a Nigeria ya sake jaddada roko kan ko an samu bayanin inda wani dan kasar da aka sace fiye da shekara daya da ta gabata yake.

Wasu 'yan bindiga ne suka sace mutumin mai suna David Priestly, mai shekara 72, kusa da Abuja, babban birnin kasar.

Har yanzu dai babu wanda ya fito ya bukaci fansa kan mutumin, kuma hukumomin Najeriya sun ce ba su san inda yake ba.

Mista Priestly ya shafe fiye da shekara 30 yana aiki a Najeriya.

Yana da mata 'yar Najeriya da kuma yara biyu.