Matsalar wuta a Afrika: Ina mafita?

Image caption Obama na son samar da wutar lantarki ga miliyoyin 'yan Africa

Wanne banbanci shirin Obama na samar da wuta a Afrika zai kawo?

A watan Fabrairu ne shugaban Amurka Barack Obama, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya don samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 50 a yankin kudu da hamadar Saharar Afrika nan da shekerar 2020.

Tambayar da Neil Ford ya yi ita ce, ko da hakan zai yiwu, mutane nawa ne kuma dai ba za su ci gaba da kasancewa cikin duhu?

Amma dai abu mafi armashi ga wannan shiri na samar da wuta a Afrika wato Electrify Africa Act of 2015, shi ne ya sanya Amurka ta kara mayar da hankali wajen kara taimakon da take yi wa kasashen duniya, a lokacin da tattalin arziki yake cikin halin rashin tabbas kuma ake samun rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa.

Shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan Amurka a jam'iyyar Repblican Ed Royce, ya hada kai da Eliot Engel dan jam'iyyar Democrat na tsawon shekara biyu don ganin kudurin dokar bai yi tasiri ba.

Kudurin dokar ya sanya gwamnatin Amurka ta goyi bayan shirin shugaba Obama na samar da wuta a Afrika.

Duk da cewa ana sa ran shirin zai lashe kimanin dala biliyan 50, hukumomin Amurka za su bayar da gudunmowar dala biliyan bakwai ne kawai.

Ana sa ran sauran gwamnatoci da hukumomin ci gaba da kamfanoni masu zaman kansu ne za su bayar da sauran kudin karkashin hadin gwiwa.

Zai yi matukar wahala a cimma hakanyayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma-baya.

Ko da a ce Amurka ta yi nasara a burinta na samar da wutar lantarki ga 'yan Afrika miliyan 50 nan da shekarar 2020, to duk da haka miliyoyin mutane da suka ninka wancan yawan sau goma ba za su samu wutar ba.

Don haka shirin samar da wutar lantarki ga Afrika ba wani dabo bane, amma a kalla ya fiddo da matsalolin rashinn isasshiyar wutar lantarki da ake fama da ita a nahiyar.

"Wutar lantarki ba abar dogaro ba ce"

Abu ne mai sauki a ki bai wa wutar lantarki muhimmanci.

Yawancin gidaje a Afrika basu da firiji ko murhun lantarki amma kwan lantarki kawai ya wadaci gidaje da yawa kuma zai bai wa yara damar yin aikinsu na gida da aka ba su a makaranta.

Image caption MA fi yawan 'yan Afrika basu da gatan amfani da murhun zamani mai amfani da wuta

Samuwar wayar sadarwa ya habaka tattalin arziki, amma rashin wutar lantarki ya sanya cajinsu ya zama wani kalubale babba.

Wani bayani da babban bankin duniya ya fitar, kashi 35 cikin 100 na al'ummar da ke zaune a yankin kudu da hamadar saharar Afrika basu da wutar lantarki.

Wannan shi ne adadi ma fi karanci fiye da kowanne yanki.

Wani yankin da mafi kashi 22 cikin 100 na al'ummarsa basu da wutar lantarki kuma shi ne yankin kudancin Asiya.

Ma fi yawan 'yan Afrika suna amfani da itace da kananzir ne wanda hakan ke jawo sare dazuka da kuma jawo dubban hadura kowacce shekara.

Mazauna yankin karkara su ne ma fi yawan wadanda suke samun wutar lantarki a gidajensu, wanda suka yi sa'ar samu tun zamanin turawan mulkin mallaka.

Wadanda suke da wutar ma kan sha wahala wajen samunta domin bata da tabbas.

Don haka masu son samunta sosai sai dai su sayi janareto.

Yayin da kasar Afrika ta kudu ta dogara da samun wutar daga makamashin kol, sauran kasashen Afrika kuwa sun dogara ne da samun wutar lantarkinsu daga ruwa.

Sai dai rashin tabbas wajen samun isasshen ruwan sama ya sanya ba kowacce shekara irin wadannan kasashe ke samun isasshiyar wuta ba, musamman ma idan akwai sauyin yanayi na El Nino.

Babbar matsalar dai ita ce rashin samun kudin shiga.

Mutane da dama basa iya biyan kudin wuta. Hakan ya sa kamfanonin rarrabar wutar basa iya samun kudaden da za a tafiyar da harkar yadda ya kamata.

Akwai bukatar ko dai arzikin mutane ya habaka ta yadda za su biya kudin wuta, ko kuma a saukaka kudin wutar.

Karin bayani