'Yan takarar Amurka za su gwada farin jininsu

Mutanen da ke son yi wa jam'iyyar Republican da ta Democrat takara a zaben shugabancin kasar Amurka za su gwada farin jininsu, yayin da jihohi 12 za su yi zaben fitar da gwani a lokaci guda.

A tsarin siyasar Amurka, ana kirar ranar ta Talata Babbar Rana, ko Super Tuesday.

Donald Trump shi ne ke kan gaba a cikin wadanda ke son yin takara a karkashin jam'iyyar Republican , yayin da Hillary Clinton I take gaba a jam'iyyar Democrat.

Tuni dai aka gudanar da zaben fitar da gwanin a jihohi hudu.

Jihar Virginia ce za ta fara yin zabe a ranar ta yau da misalin karfe11:00 a agogon GMT.

Mrs Clinton tana sa ran ci gaba da samun nasara bayan nasarar da ta yi a jihar South Carolina a karshen makon jiya.

A ranar takwas ga watan Nuwamba ne 'yan Amurka za su zabi mutumin da zai maye gurbin Shugaba Barack Obama a fadar White House.