Za a nemo mutanen da suka tsere a Zamfara

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce za ta jagoranci wata tawaga da za ta zagaya kauyuka daban-daban na jihar Zamfara domin tattaro daruruwan iyalan da suka arce daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan fashin shanu.

Babban jami'i mai kula da aikace-aikacen hukumar a shiyyar Sakkwato, Mr. Thickman Tanimu, ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza cewa yawancin mutanen 'yan karamar hukumar Maru ne:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dubban mutane ne rahotanni suka ce sun nemi mafaka a wasu garuruwan da ke makwabtaka da kauyukan nasu sakamakon karuwar hare-haren a watannin bayan nan da suka lakume rayukkan fiye da hamsin.

Wannan dai na zuwa ne bayan a yau hukumar ta NEMA ta rufe wani sansani inda wasu 'yan gudun hijirar kimanin 500 suka fake tsawon kwana 17 a babban birnin jihar Gusau.