Mujuru ta kafa jam'iyya a Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto AFP

Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Zimbabwe, Joice Mujuru, ta kaddamar da jam'iyyarta sama da shekara daya bayan Shugaba Robert Mugabe ya kore ta daga mukaminta.

A wani taron manema labarai, ta bayyana kasar a matsayin kasar da komai n ta ya tabarbare.

Joice ta ce sabuwar jam'iyyar -- Zimbabwe People First -- ba yaki take yi da mutum guda ba amma tana yaki ne da rashin adalci da ake yi a kasar baki daya.

A lokacin da take mayar da martani a kan cin mutuncin da matar shugaba Mugabe, Grace, take mata, Misis Mujuru ta ce ita ba mayya ba ce, kuma ba mai kisan kai.