Tarayyar turai za ta taimaki Girka

Baki 'yan cirani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yawancin 'yan ciranin sun fito ne daga yankin gabas ta tsakiya.

Kungiyar tarayyar Turai na shirin kashe miliyoyin daloli a kan ayyukan agaji cikin shekaru uku masu zuwa don taimaka wa kasar Girka a dawainiyar da take yi da dubban 'yan ci-rani da masu gudun-hijirar da ke kwarara kasar.

A karkashin shirin, wanda ake sa ran gabatar wa Hukumar tarayyar Turai za a dinga samar da kudin aikin agajin ne a cikin Tarayyar Turai kamar yadda ake yi wajen magance rikici a sassan duniya da ke fama da tashin hankali.

Idan wannan kudurin ya samu amincewa, to hukumomin agaji na Tarayyar Turai, a karon farko za su dinga yin aiki da majalisar dinkin duniya kai-tsaye, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da ke Turai, maimakon danka kudi ga hannun gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar, kamar Girka.