An gano kwayar halittar da ke sa furfura

Ana danganta mai furfura da tsufa. Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Yawancin masu furfura kan shafa shuni ko lallae a gashinsu dan ya sauya launi.

Masana kimiyya, a karon farko, sun gano kwayar halittar da ke jikin dan'adam da ke saka shi yin furfura, wata alamar da a wani lokaci ake dangantawa da tsufa.

Masanan sun ce wata kwayar halitta da ake kira IRF4 ce ke daidaita sinadarin melanin a jikin mutum, kuma melanin din ne ke daidaita launin gashi da na ido da kuma fatar jiki.

Sun ce binciken zai taimaka wajen samun hanyoyin jinkirta furfura, ko hana ta bulla a jikin mutum baki daya.

Sai dai binciken ya bayyana cewa ba kwayar halittar ce kadai ke haddasa furfura ba, akwai wasu dalilai, ciki har da wahala da kuma shiga yanayi na tashin hankali.

An dai wallafa sakamakon binciken ne a cikin mujallar Journal Nature Communications, kuma an gudanar da binciken ne a kan samfurin kwayar halittar da aka cira daga jikin sama da mutum 6000 da suka fito daga Turai da Amurka da kuma Afirka.