Masu neman aikin soji sun yi zigidir a India

Hakkin mallakar hoto BiharphotoGopi Raman Mishra
Image caption Irin yadda aka sa masu zana jararabawar suka tube kenan

An sanya daruruwan matasa masu neman aiki sun cire tufafinsu a jihar Bihar da ke Indiya, domin a yi musu gwajin daukar aikin soji a wani mataki na hana cuwa-cuwa.

Wasu hotuna sun nuna yadda masu neman aikin suke zaune sun tankwashe kafufunsu a wani fili da ke garin Muzaffarpur, inda suke sanye da gajerun wanduna kawai.

Sojoji sun ce an yi hakan ne domin a rage lokacin da ake diba don bincikar dalibai da dama.

Wani daga cikin masu neman aikin ya ce, "Gaskiya hakan bai dace ba."

Jami'ai sun ce mutane 1,159 ne suka zana jarrabawar shiga aikin soji da aka shafe tsawon sa'o'i ana yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Karin bayani