'Yan kasuwa na son CBN ya sake tsarin bada kudin waje

Kudaden kasashen waje Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kudaden kasashen waje

Wani hamshakin dan kasuwa a Nigeria, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u, da ke shugabantar rukunin kamfanin BUA, ya yi kira ga gwamnatin Nigeria da ta duba yadda Babban bankin kasar CBN ke bayar da kudaden kasashen waje ga jama'a da kuma kamfanoni.

Wannnan kira ya zo ne a yayin da tattalin arzikin Nigeria ke fuskantar matsaloli saboda faduwar farashin Man Fetur a kasuwannin duniya.

Babban bankin Nigeria dai ya yi ikirarin cewar baya bayar da kudade ga jama'a illa ta hanyar bankunan kasar.

A kwanakin baya ne dai Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u, ya bayyana cewar matsalar karancin kudaden wajen ta na neman tilasta musu rufe kamfanonin su.