Najeriya da Turkiyya za su yaki ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Nigeria Government
Image caption Shugabannin biyu sun kuma sanya hannu kan hada kai ta fuskar tattalin arzikin

Shugabannin kasashen Najeriya da Turkiyya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin kai ta fuskar tattalin arziki da ciniki da habbaka masana'antu da kuma yaki da ta'addanci.

Muhammadu Buhari da Rajib Tayyib Erdogan sun cimma yarjejeniyar, bayan wata doguwar tattanawa da suka yi a fadar shugaban Najeriya da ke birnin tarayya Abuja.

A daren Talata ne dai Shugaba Edowan ya isa Najeriya daga kasar Ghana domin yin wata ziyara ta kwanaki uku.

Kasashen biyu sun sha fuskantar hare-haren ta'addanci, abinda ya sa a yanzu suka sha alwashin hada gwiwa don yakar matsalar.

Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya yi wa Sulaimanu Ibrahim karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti