Koriya ta Arewa ta harba makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kakakin rundunar sojin Koriya ta Kudu ya ce sun ga yadda aka harba makaman.

Korea ta Arewa ta harba makamai masu cin karamin zango guda shida a gabar teku da ke kudancin kasar a wani martani game da sabon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ya sanya mata.

Kakakin rundunar sojin Koriya ta Kudu, Moon Sang-Gyun, ya ce sun ga yadda aka harba makaman, sai dai ba su fada kan wurin da aka hara ba.

Ya ce, "Sojojin Koriya ta Arewa sun harba makamai masu cin karamin zango wanda ya fada a gabar tekun da ke kudancin kasar da misalin karfe daya a agogon GMT, kuma jami'an sojinmu na cikin shirin ko-ta-kwana.

Masu lura da al'amura sun ce akwai yiwuwar a samu karuwar zaman dar-dar a yankin sakamakon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa Koriya ta Kudu saboda gwajin da ta yi na makamin nukiliya a watan Janairu.