'Yan Shia sun kaurace wa kwamitin bincike

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Shia sun bukaci a sako Sheikh Al-Zakzaky.

'Yan Shi'a sun ce ba za su sake halartar zaman kwamitin da ke bincike don gano dalilan da suka sa aka yi arangama tsakani sojoji da 'yan kungiyar.

Arangamar dai ta faru ne bayan sojoji sun yi zargin cewa mabiya Shia sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan rundunar Sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai a lokacin da kai ziyara garin Zaria a karshen shekarar da ta gabata, ko da ya ke 'yan kungiyar sun musanta zargin, kuma lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

'Yan kungiyar dai sun ce sun dauki matakin daina halartar zaman kwamitin har sai an sako shugabansu, Sheikh Ibrahim Al-Zazzaky, da wasu 'yan kungiyar da ake tsare da su.

Dr Abdullahi Danladi shi ne ya jagoranci 'yan kungiyar wajen yin taron manema labarai, kuma ya shaida wa BBC cewa, "Lauyoyinmu sun yi dukkan kokari domin su ga Malam Al-Zazzaky, amma abin ya ci tura. Don haka ne muka yanke hukuncin cewa ba za mu sake halartar wajen zaman da kwamitin da jihar Kaduna ta kafa ba, har sai an sake shi."

A cewarsa, "Wadanda ke tsare a gidan yari yawancinsu dalibai ne, kuma basu da lafiya. Wasu ma suna da raunuka na harsashi, wasu kuma sassan jikinsu suna rubewa."

Sai dai tun lokacin da kwamitin ya fara aikinsa, shugabansa Justcie Muhammad Lawal Garba, ya ce aikinsu shi ne su gudanar da bincike kan abin da ya faru, ba shari'a za su yi wa kowa ba.