Dangantakar Nigeria da Turkey

Hakkin mallakar hoto Nigeria Goverment
Image caption Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Nigeria da Turkiya

Bayan da Nigeria ta samu 'yancin kai a shekarar 1960, sai Turkiya ta bude ofishin jakadancinta a Lagos, babban birnin kasar a wancan lokaci, cikin watan Agustan 1962.

Daga baya ofishin jakadancin Turkiya ya dawo Abuja a shekarar 2001, bayan da ta zama sabuwar birnin tarayyar kasar a shekarar 1991.

Ita ma Najeriya tana da nata ofishin jakadancin a Ankara, babban birnin Turkiya.

Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Turkiya da Najeriya musamman ta fuskar siyasa.

Dukkan kasashen biyu suna da manufar siyasa ta kyautata alakarsu a dukkan bangarori.

Najeriya da Turkiya mambobi ne na kasashe takwas masu tasowa D-8, kuma akwai kyakkyawan hadin kai tsakaninsu a kungiyoyin kasa da kasa.

Sakamakon ziyarorin da kasashen biyu suka kai wa juna a baya-bayan nan kamar ziyarar shugaban kasar jamhuriyyar Turkiya Mista Abdullah Gül, zuwa Najeriya a watan Yulin 2010, da ta tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, zuwa Turkiya a watan Fabraitun 2011, an samu hadin kai kan sabbin damarmaki ta bangarori da dama tsakanin kasashen biyu.

An kuma cimma yarjejeniyoyi da dama ta bangaren siyasa da aikin soji da tattalin arziki da ala'du da kuma ilimi.

Image caption Shugaba Jonathan ma ya sake kulla alakar kasuwanci da Turkiya a lokacin mulkinsa
"Kasuwanci"

Dangantakar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu na karuwa a hankali.

Kazalika, hada-hadar kasuwancin kasashen ta ribanya sau uku tun shekarar 2004, inda ya kai dala miliyan 865 a shekarar 2010.

Ana harkar kasuwanci a duk shekara tsakanin wadannan kasashe na kimanin dala miliyan 32.6, inda Najeriya ke shigo da tufafi da abinci da injina da motoci da kuma magunguna. Ita ma Turkiya na shigar da irin ridi da man fetur da fatu da kiraga da kuma robobi daga Najeriya.

Najeriya ita ce kasa ta biyu da tafi mu'amalar kasuwanci da Turkiya a yankin kudu da hamadar saharar Afrika tun daga shekarar 2010.

Akwai a kalla kamfanoni 30 na kasar Turkiya a Najeriya, wadanda suke aikinsu kan harkokin gine-gine da masana'antu da kuma makamashi.

"Harkar Ilimi"

Turkiya ta kuma samar da gurbin karo karatu kyauta na mutum 55 ga Najeriya karkashin wani shirin gwamnatinta tsakanin shekarar 2008 da 2011.

Akwai makarantun firamare da sakandare da jami'a na kasar Turkiya da ke bayar da ilimi a Najeriya ga fiye da dalibai 3500.

"Sufuri"
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin jiragen sama na Turkiya na zirga-zirga daga Istanbul zuwa Najeriya

Kamfanin jiragen sama na Turkiya ya fara zirga-zirga kai tsaye tsakanin Lagos zuwa birnin Istanbul a watan Yulin 2006, a yanzu haka kuma jirage hudu ne suke zarya a kowanne mako.

"Kamanceceniya"

Akwai al'amuran da Najeriya da Turkiya suke kamanceceniya da juna ta harkar zamatakewa, duk da bambancin a tarihinsu.

Abubuwa kamar tsadar rayuwa da cin hanci da sauransu, wadanda suka mamaye al'muran rayuwar 'yan Najeriya da Turkiya.

A bangaren manufofin harkokin waje na kasa kuwa, Najeriya da Turkiya dukkansu kasashe ne masu karfin iko a yankunansu, a dalilin haka ne suke da dabarun manufofin harkokin waje iri daya, suke kuma fuskantar kalubale daga bangarori daban-daban a duniya.

Hakkin mallakar hoto Nile University

Kazalika, wani abu da ya kara sanya kusanci tsakanin Turkiya da Najeriya shi ne kasancewar dukkansu suna da dumbin yaruka daban-daban a kasashen.

Haka kuma Turkiya kasa ce ta Musulmai, kuma rabin al'ummar Najeriya ma musulmai ne.

Wadannan da ma sauran abubuwa da dama na daga cikin dalilan da suka sa dangantakar kasashen take da karfi tun da dadewa.