Erdoğan na yin ziyara a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Goverment
Image caption Erdogan ya gana da Shugaba Buhari.

Shugaban kasar Turkiyya, Reccep Tayyip Erdogan, ya sauka a filin jirgin saman Abuja, inda ya fara ziyara a kasar.

Mista Erdogan, wanda ya sauka a Najeriya bayan ya kammala irin wannan ziyara a kasar Ghana, ya samu tarba daga wajen ministar harkokin waje ta kasar Khadija Bukar Abba Ibrahim, da takwaranta na birnin tarayya, Mohammad Musa Bello da kuma jakadan Turkiyya a Najeriya, Hakan Çakıl.

Tuni dai shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana da takwaransa na Turkiyya.

Ana sa ran kasashen biyu za su tattauna a kan batutuwa da dama ckinsu har da tattalin arziki da tsaro.

Cikin wadanda ke yi wa Shugaba Erdoğan rakiya har da matarsa, Emine Erdoğan, da ministan harkokin waje, Mevlüt Çavuşoğlu, da ta Muhalli, Fatma Güldemet Sarı, da na tattalin arziki Mustafa Elitaş, da na makamashi, Berat Albayrak, da na tsaro İsmet Yılmaz da kuma manyan 'yan kasuwar kasar.

'Dangantaka tsakaninsu'

Alkaluma sun nuna cewa kasuwancin da ke tsakanin Najeriya da Turkiyya ya wuce na Dala biliyan biyu.

Kazalika, kasashen na cikin kungiyar kasashe takwas masu ci gaba da kuma kasashen kungiyar MINT -- Mexico, Indonesia, Nigeria da Turkiyya -- wadanda ake hasashen tattalin arzikinsu zai bunkasa nan da shekara 20.

Turkiyya dai tana da makarantu a Najeriya, cikinsu har da Jami'a da kwalejoji.

Haka kuma Najeriya tana shigowa da darduma daga Turkiyya, yayin da ita kuma Turkiyya ke watsa labarai da harshen Hausa.