An dakatar da Galatasaray daga kwallo

Hakkin mallakar hoto UEFA

Hukumar kwallon kafar Turai, UEFA, ta dakatar da kungiyar kwallon kafar daga shiga gasar cin kofin Turai har tsawon shekara daya.

An dauki matakin ne bayan kungiyar kwallon kafar ta kasar Turkiyya ta gaza wajen kiyaye ka'idojin da aka sanya wa kungiyoy na kashe kudi.

A baya dai UEFA ta ce Galatasaray bata ki ka'idojin da aka kafa kan kashe kudi.

Galatasaray ta lashe gasar league ta Turkiyya a shekarar da ta gabata, sai dai ta gaza yin katabus a bana.