Trump da Hillary sun ci gaba da yin nasara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mrs Clinton ta lashe jihohi takwas.

Donald Trump da Hillary Clinton sun yi nasara a yawancin jihohin da suka yi zaben fitar da gwani na wadanda ke son yi wa Republican da Democrat takarar shugabancin Amurka.

A jam'iyyar Republican, Mr Trump ya lashe zaben jihohi bakwai yayin da mai biye masa, Ted Cruz, ya yi nasara a jihohi uku. Shi kuwa Marco Rubio, ya yi nasara a jiha daya.

Mr Trump ya sha kaye a hannun Sanata Ted Cruz a jihohin Texas da Okhahoma.

Da yake jawabi a jiharsa ta Texas, Mr Cruz ya bukaci sauran masu son yin takara a karkashin jam'iyyar su fita daga takarar, sannan su mara masa baya domin ya kayar da Mr Trump.

Image caption Mr Trump ya lashe jihohi bakwai, yayin da Mrs Clinton ta lashe jihohi takwas.

Mrs Clinton ta lashe jihohi takwas.

Mutumin da ke son yi wa jam'iyyar Democrat takara, Bernie Sanders, ya samu nasara jihohi huhu, cikinsu har da jiharsa ta Vermont.

Tuni dai magoya bayan masu neman takarar suka fara bayyana fatan nasara ga gwanayen nasu.