Kun san kasashen da suka fi fama da rashin aiki?

Image caption Nahiyar Afirka na cikin wadanda suka fi fama da marasa aikin yi.

A wannan makon ne kasar China ta ce akwai yiwuwar za ta kori ma'aikata miliyan daya da dubu 800 daga aiki saboda tabarbarewar tattalin arziki.

Image caption Tabarbarewar tattalin arzikin Turai ya ta'azzara matsalar

Marasa aikin yi ba su da yawa a kasar kuma duk da shirin rage yawan ma'aikatan, kasar ta China ba za ta shiga cikin jerin kasashen da suke fama da matsalar rashin aikin yi ba.

A wannan rahoton, wakiliyarmu, Valeria Perasso ta duba lokuta mafi muni da aka yi fama da rashin aikin yi.

Alkaluman tattalin arziki na baya bayan nan da China ta fitar sun tabbatar cewa tattalin arzikin kasar yana ci gaba da tabarbarewa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran za a kori ma'aikatan kwal miliyan daya da dubu 800 a China.

Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai da Reuters ya fitar ya ce kusan mutane miliyan daya da dubu 800 da ke aiki a ma'aikatar kwal da karafuna, wadanda su ne kashi 15 cikin dari na yawan ma'aikata, za su rasa aikinsu, a wani bangare na kokarin rage cunkuson mutane a ma'aikatu sakamakon raguwar aikace-aikace a masana'antun kasar.

An yi amanar lardunan da suke samar da gawayi da karafuna su ne za su fi shan wahala.

Amma menene girman matsalar da China take hange?

Samar da aikin yi na daga cikin muhimman manufofin gwamnatin China kuma marasa aikin yi a kasar basu da yawa.

Ko da yawan marasa aikin yi ya kai kusan miliyan biyu, China ba za ta kasance cikin kasashen da ke fama da rashin aikin yi ba, idan aka yi la'akari da cewar gaba daya ma'aikatan kasar su miliyan 806 ne, wanda ya fi ko wanne yawa a duniya, kuma ya kusan ninka na Indiya, wacce ita ce ta biyu a alkaluman da bankin duniya ya fitar.

Hasalima, kasashe120 sun fi China fuskantar yawan marasa aikin yi.

'Kasashen da suka fi yawan marasa aikin yi'

Don haka, wadanne kasashe ne suka fi yawan marasa aikin yi?

Ga guda goma da suka fi yawan marasa aikin yi:

Kasashen Afirka, musamman na kudanci da yammacin nahiyar da kuma kasashen yankin Mediterranean su ne kan gaba a yawan marasa aikin yi, idan aka yi la'akari da alkaluman da kungiyar kwadago ta duniya ta fitar a shekarar 2014.

Matsalar rashin aikin yi a Afirka

Mauritania ce ke kan gaba a yawan marasa aikin yi, inda ta kwashe fiye da shekara goma tana da kashi 30 cikin dari na marasa aikin yi, inda marasa aikin yin ta ya kai kashi 32.8 a shekarar 2004.

Masana sun dora alhakin hakan a kan matsalolin tattalin arziki, cikin su har da matsanancin farin da ta fuskanta a shekarar 2012, wanda ya yi illa ga tattalin arzikinta sannan matasa suka rasa aikin yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dalibai a Afirka ta kudu sun yi zanga-zanga saboda karin kudin makaranta.

Afirka ta kudu ce ta uku da ta fi yawan marasa aikin yi a Afirka.

Alkaluman da kungiyar tattabar da mulki na gari ta Good Governance Africa (GGA) ta fitar sun nuna cewa matasan Afirka ta kudu sun fi kowa fuskantar yiwuwar rasa aiki idan suka kammala karatu.

Tabarbarewar tattalin arzikin Turai

Tabarbarewar da tattalin arzikin duniya ya fara yi a shekarar 2007 ya kara yawan marasa aikin yi daga miliyan 178 a shekarar 2007 zuwa miliyan 212 a shekarar 2009, a cewar kungiyar kwadago ta duniya.

Hakan ya yi gagarumin tasiri a nahiyar Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyoyin kwadago a Girka sun yi zanga-zanga a birnin Athens domin hana a rage yawan albashinsu a watan Disambar shekarar 2015.

Kasashen da wannan matsala ta fi yin karami su ne Girka da Spain.

Ita ma kasar Bosnia da Herzegovina tana cikin wadanda ke fama da wannan matsala, kuma an danganta haka ne da yakin da aka yi a Bosnia, wanda aka gama a shekarar 1995.

Matasan Bosnia-Herzegovina su suka fi fama da rashin aikin yi a duniya, musamman saboda matsalar cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

Macedonia ta taba zama kasar da ta fi yawan marasa aikin yi a cikin kasashen da suka kafa tsohuwar kasar Yugoslavia. Ta kwashe shekara da shekaru tana fama da matsalar duk da cewa tattalin arzikinta yana bunkasa, inda ake ganin rashin aikin yin ya faru ne saboda tsarin kasar.