'Za a hana shigar da kayan gwanjo a gabashin Afrika'

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutane dama a Afrika na sayan kayan gwanjo da ake kawowa daga Turai da Amurka.'

Amma kasashen gabashin Afrika na kokarin hana shigowa da gwanjon kayan sakawa da gwanjon motoci a shekaru uku masu zuwa, abin da zai kawo karshen kasuwanci mai riba a yankin.

Wa ke so ya hana gwanjon kayan sawa da na motoci?

Burundi da Kenya da Rwanda da Tanzania da kuma Uganda duk za su iya hana shiga da gwanjon kayan sakawa da fatu zuwa kasashensu.

Su ne kasashen kungiyar gabashin Afrika watau EAC a takaice.

EAC ta bayar da umarni kasashen su sayi tufafi da takalma a cikin yankuna da zummar hana shigowa da zuwa shekarar 2019.

Kafin taron na ranar Laraba, EAC ta kuma bayar da shawarar rage shigowa da gwanjon motoci.

Yaushe za a hana?

EAC din ta bayar da shawarar hana shigowa da kaya a cikin shekaru uku masu zuwa.

Duk da haka jaridar gabashin Afrikar ta rawaito cewar ya danganta da shugabannin kasashen guda biyar su yarda a kan manufar masana'antu.

Jaridar ta kara da cewar shawarar hana shigowa da gwanjon zai soma aiki ne bayan an samu karuwar samar da tofafi a kasashensu.

Me yasa suke so a daina shigowa da gwanjo?

An yanke wannan shawara ce domin a bunkasa masaku a kasashen da zummar bunkasa tattalin arzikin su.

Sai dai abu daya da ake musu a kai shi ne, kayan gwanjo suna da matukar arha ta yadda masanantu samar da tufafin kasashen da kuma teloli ba za su iya samar da kayan da araha kamar na gwanjon ba, saboda haka ko dai su rufe ko basa yi da kyau kamar yadda ya kamata.

Wani rahoto da EAC ta fitar a taron masanantu da kasuwanci na kasashen guda biyar, ya ce, masana'antun fata da tufafi suna da matukar muhimmanci wajen samar da aikin yi da rage talauci da kuma ci gaban samar da fasaha a yankin.

Gwanjo suna da illa ga lafiya?
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwanjon kayayyaki irinsu fatari da rigar mama da kuma kamfai an dauke su a matsayin ba su da tsafta.

EAC din ta bukaci gwamnatoci su tabbatar cewar gwanjon kaya suna bin ka'idojin tsaftar tufafi.

Kasar Ghana ta hana shigowa da gwanjon kamfai a shekarar 2011 kuma wani kudirin doka a kasar Uganda ya yana shigowa da gwanjo a shekarar da ta gabata.

An dora alkhakin yawan hatsarin mota a kan tsaffin motoci.

Wani mai sharhi na sashen Swahili na BBC, Alex Mureithi ya yi bayanin cewar, saboda kaucewa biyan haraji, mutane suna bayar da cin hanci a tashoshi jiragen ruwa domin shigowa da gwanjon motoci.

Don haka ba a duba lafiyar wadannan motoci.

Domin sannin yadda fasa kaurin kayayyaki da ake shigowa da su, ya bayyana a cikin watan Disamba cewar sama da jiragen ruwa na daukar kaya dubu 2,700 sun bata a tashar jirgin Dar es Salaam da ke Tanzania.

Shin ana yawan sa Gwanjo?

A kasar Uganda, gwanjo kaya su ke samar da kashi 81 cikin 100 na tufafin sayarwa, in ji Andrew Brooks a littafin sa mai suna talaucin tufafi.

A wasu alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar, daga shekarar 2013, Koriya ta Kudu da Canada sun fitar da gwanjon kaya da darajarsu ta kai dala miliyan 59 zuwa Tanzania, yayin da Ingila kadai ta fitar da gwanjon kayan da darajarsu ta kai dala miliyan 42 zuwa Kenya.