Dalibi dan Masar ya yi barazanar kashe Trump

Hakkin mallakar hoto Cairo post
Image caption Dalibi Emadeldin Elsayed

Wani dalibi dan kasar Masar na fuskantar yiwuwar mayar da shi kasarsa daga Amurka saboda wata barazana da ya yi a shafinsa na Facebook, cewa yana burin kashe dan takarar shugabancin Amurka, Donald Trump.

Emadeldin Elsayed, mai shekara 23, ya ce in har ya yi hakan ya san ko duniya ma za ta yi masa godiya.

A yanzu dai ba a tuhumi Elsayed da aikata wani mugun laifi ba sakamakon sakon, amma jami'an shige da fice sun kama shi a watan da ya gabata.

Yanzu dai za a gurfanar da shi a gaban shari'a don yanke masa hukuncin ko za a mayar da shi kasarsa.

Mista Elsayed ya ce ya rubuta sakon ne, saboda yana jin takaicin irin kalaman da Mista Trump ke yi a kan Musulmai.

Sai dai ya kara da cewa tuni ya yi dana sanin hakan, kuma tun da farko bai yi da nufin zai cutar da kowa ba.

Karin bayani