Karancin man fetur ya addabi 'yan Nigeria

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan bunburutu na cin karensu babu babbaka

Karancin man fetur na ta'azzara a sassa daban-daban na Nigeria, inda ake samun dogayen layuka a gidajen mai.

Wannan al'amari har ya sa wasu daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama na kasar sun tsayar da jigilar fasinjoji.

Wannan matsala dai tafi shafar kamfanin jiragen sama na Arik.

Rahotanni na cewa tuni wasu gidajen man suka kara farashin lita daga naira 87 zuwa naira 120 har 150 a wasu wuraren.

Har zuwa yanzu dai hukumomin da ke da alhakin samar da man ba su ce komai ba kan batun.

Sai dai lamarin ya sanya mutane cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, ta yadda har farashin wasu abubuwan amfanin yau da kullum sun fara farashi.

Karancin man fetur dai wani lamari ne da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriyar, duk kuwa da cewa an samu sabuwar gwamnatin da mutane ke ganin za ta iya kawo karshen ta baki daya.