Google ya bada gudummuwa don yaki da Zika

Hakkin mallakar hoto
Image caption Google ya na bada bayanai ta Internet game da cutar Zika

Sashen da ke bada tallafi a Kamfanin Google ya ba Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, wato UNICEF gudummuwar dala miliyan daya don hana yaduwar kwayar cutar Zika.

Annobar cutar da aka alakanta da haifuwar gilu watau jariri mai karamin kai ta bulla ne a kasar Brazil.

A watan Fabrairu ne Hukumar lafiya ta Duniya ta ayyana cutar ta Zika a matsayin annoba da ake bukatar agajin gaggawa a kanta.

Kamfanin na matambayi-ba-ya-bata, wato Google ya kuma gyara hanyar neman bayanai ta Internet ta yadda za'a rika fitar da muhimman bayanai game da cutar Zika da aka wallafa a harsuna 16 ga baki da ke zuwa Amurka da kuma wasu kasashe.