'Adam Johnson ya ba mu kunya' —Allardyce

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adam Johnson a Sunderland lokacin da tauraruwarsa ke hasakakwa kafin abin kunyarsa na lalata da 'yar shekara 15

Amsa laifin da Adam Johnson ya yi na lalata da wata yarinya ya matukar girgiza Kociyan Sunderland Sam Allardyce.

An rawaito kociyan na cewa "wannan ba karamin tashin hankali ba ne, an riga an yanke hukunci, ya kuma ba mu kunya".

Adam Johnson dan shekaru 28, yana fuskantar zaman gidan yari bayan da aka same shi da laifin lalata da yarinya 'yar shekara 15.

Dan kwallon ya na bugawa Sunderland ne kafin soma shari'arsa, amma aka kore shi bayan amsa wasu tuhume-tuhume guda biyu a ranar farko na shari'ar lalata da wata yarinya 'yar shekara 15.