Kamfanin Jumia ya samu farin jini a duniya

Babban kamfanin sayar da kayayyaki ta shafukan intanet a Najeriya mai suna Jumia, ya ce ya samu nasarar samun masu zuba jari daga kasashen duniya hudu.

Kasashen sun hada da Faransa, da Jamus, da Afrika ta Kudu da Amurka, wadanda suka kagu su zuba jari a kamfanin.

Kamfanin na Jumia ya ce, jarin da za a zuba zai kai dalar Amurka miliyan 325, wanda hakan zai sa jimillar jarin kamfanin ya zarta dala biliyan daya.

Kamfanonin da za su zuba jari a kamfanin na Jumia da ke hada-hadarsa a Najeriya sun hadar da Bankin zuba jari na kasar Amurka Goldman Sachs, da Kamfanin Inshora na Faransa AXA, da kamfanin Racket na kasar Jamus da kuma kamfanin wayar salula na MTN.

An dai kafa kamfanin Jumia a Najeriya ne a shekarar 2012, domin ya bayar da dama ga masu samar da kayayyaki a nahiyar Afrika su rika sayar da kayayyakinsu a shafukan intanet.