Rikici: An rufe kasuwar Mile-12 ta Lagos

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An tura jami'an tsaro domin kwantar da rikicin

Gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode ya bayar da umurnin rufe kasuwar 'Mile 12' da ke unguwar Ketu, a jihar domin kwantar da kurar rikicin da ya tashi.

Sanarwar da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta ce rufe kasuwar na wucin gadi ne domin kawo karshen tashin hankalin da aka samu.

Matakin na gwamnan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin 'Area Boys' wadanda galibinsu Yarbawa ne, da kuma 'yan acaba wadanda galibinsu Hausawa ne 'yan arewacin kasar.

Wasu rahotanni sun ce an halaka akalla mutane uku a rikicin wanda aka soma shi tun a ranar Talata.

Wakilinmu na Lagos ya ce an tura karin jami'an tsaro domin kwantar da lamarin.

Rikicin kabilanci wani al'amari ne da yake addabar sassa daban-daban na Najeriya.