MTN ya fada mawuyacin hali

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da sakamakon hada-hadar da ya yi daga ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Sakamakon ya bayyana irin yanayin wahalar da kamfanin ya ke kasuwanci a ciki a lokacin da aka yi nazari.

Harkokin kasuwanci kamfanin a Najeriya sun fuskanci kalubale da dama a shekarar.

Tabarbarewar yanayin tattalin arzikin da kuma takaitar samuwar dalar Amurka ya taimaka wajen rashin inganci a kasuwancin kamfanin.

Matsin lambar hukumar sanya ido kan harkokin kamfanonin sadarwa ya yi mummunan tasiri a kan kamfanin na MTN da ke Najeriya.

Babban abin da ya ta'azzara halin da MTN ya fada a ciki shi ne tarar da gwamnatin Najeriya ta ci shi ta sama da Naira Tiriliyan daya sakamakon kin yanke layukan wasu masu amfani da shi har wa'adin yin rijista ya wuce.

MTN ya biya Naira biliyan dari biyar.