Sabon tsarin rabon kayan agaji a Jihar Nasarawa

Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Almakura ya ce sun koyi darasi kan raba kayan agaji a jihar.

Gwamnatin jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya ta fitar da wani sabon tsarin rabon kayan agaji ga al'umomin da suka yi fama da rikice-rikice a jihar, bayan ta samu korafin cewa kayan ba sa isa hannun wadanda ake yi dominsu.

A baya dai gwamnatin ta shafe kusan shekara uku tana amfani ne da wasu sarakunan gargajiya da kuma shugabannin siyasa, wadanda aka yi ta danka musu kayan agaji na miliyoyin Nairori.

Akalla al'umomi talatin daga kauyuka kusan hamsin ne suka yi fama da rikice-rikice masu nasaba da kabilanci, da addini da kuma siyasa a jihar Nasarawar, lamarin da ya daidaita su, inda suka fada cikin kuncin rayuwa.

Gwamnatin jihar dai kan yi ikirarin tallafa musu da kayan agaji da ya hada da abinci da tufafi da kayan daki da kuma magunguna, amma a cewar al'umomin ba sa gani a kasa, don haka abin da suka sani shi ne rijiriya na ba da ruwa amma guga na hanawa.

Sai dai Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Almakura ya ce abin takaici ne yadda ake ha'intar mabukatan inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta koyi darasi, kuma ta rungumi sabon tsarin raba kayan agajin.

A halin yanzu gwamnatin jihar ta sake tanadin kayan agaji na sama da naira miliyon dari biyu da za ta raba bisa sabon tsarin tare da samar da wasu asibitocin tafi-da-gidanka su uku, wadanda ciki har da wurin yin tiyata, wadanda za a kai su cikin al'umomin da suka yi fama da rikicin don kula da lafiyarsu zuwa lokacin da za a sake gina musu asibitoci.