OPEC za ta gana kan wasu matsaloli

Hakkin mallakar hoto

Wasu mambobin kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur na OPEC suna shirin yin wata ganawa da wasu kasashen masu hako man a Rasha a 20 ga watan Maris.

A ranar Alhamis ne Ministan mai na Najeriya, Ibe Kachikwu, ya ce ganarwa za tattauna ne a kan toshe wata hanyar fitar da mai.

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, ministan ya ce, "Mun fara ganin farashin mai yana dan hawa a hankali. Amma idan har wannan ganawa da muke shiryawa, wadda muke sa ran za a yi a Rasha tsakanin kasashen da suke hako mai na OPEC da wadanda ba na OPEC ba a 20 ga watan Maris, za mu samu sauyi a farashin man".

Kasar Iran, wacce aka cire wa takunkumi, ta ce za ta ci gaba da hako manta na fetur.