Romney da McCain sun yi tir da takarar Trump

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mitt Romney ya bayyana Trump a matsayin dan damfara

Biyu daga cikin manyan kusoshin jam'iyyar Republican a Amurka, Mitt Romney da John McCain, sun yi Allah wadai da dan takarar fidda gwani na jam'iyyarsu da ke kan gaba, Donald Trump.

Mr Romney ya bayyana Mista Trump din da cewa dan damfara ne, makaryaci, wanda ya tsani mata, wanda kuma bai cancanci ya jagoranci Amurka ba.

Mitt Romney ya ce yana wasa da hankalin Amurkawa ne kawai, wato kamar ace a tura mota ne kawai ta kai shi fadar White House ya bida muku kura ya yi gaba.

Mr McCain ya bayyana damuwa game da yadda yake fuskantar batun tsaron kasar Amurkar a jahilce, kuma a cikin hadari.

Wadannan kalaman na nuna irin fargabar da ake da ita a jam'iyyar Republican yayin da Mr Trupm ke dab da samun nasarar tsayawa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar.