'An kashe mutum 50,000 a Sudan ta kudu'

Hakkin mallakar hoto REUTERS

Wani babban jam'in majalisar dinkin duniya ya ce an kashe akalla mutum 50,000 a yakin basasar da aka yi a Sudan ta kudu.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce alkaluman sun nuna cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya ninka sau biyar na wadanda hukumomin agaji suka fitar a watannin farkon yakin.

Jami'in ,wanda ba ya so a fadi sunasa, ya shaida wa wasu manema labarai cewa, "An kashe mutum 50,000, ko ma fiye da haka, sannan yakin ya raba mutum miliyan biyu da dubu 200 daga muhallansu, yayin da fari ke kunno kai a watanni kadan masu zuwa."

Yankin basasar da ake yi a Sudan ta Kudu, wadda ita ce kasa mafi kankantan shekaru, ya fara ne a watan Disambar shekarar 2013 bayan Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki.

Sai dai Mista Machar ya musanta zargin amma kuma ya kafa sojojin sa kai.

An kuma zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa bayan sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Agusta bayan an yi barazanar sanya musu takunkunmi.