Ba wutar lantarki dungurugum a Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Yakin Syria da ya ki ci ya ki cinyewa na jawo matsaloli daban-daban

Syria na fama da matsanancin rashin wutar lantarki a baki daya kasar, sakamakon wasu dalilai da ba a san su ba.

Jami'ai sun ce an yanke wutar a dukkan yankunan kasar kuma ma'aikata na ta kokarin gano dalilin da ya jawo hakan.

Ma'aikatar wutar lantarki ta kasar ta ce an shawo kan matsalar kuma wutar za ta samu cikin daren Alhamis.

Tuni dai dama wutar lantarki ta yi karanci a mafi yawan wurare a Syria, musamman inda yaki ya fi kamari, ta yadda ake samun wutar sa'o'i biyu zuwa hudu kacal a rana.

Sai dai kuma da wuya ake samun irin wannan dauke wuta ta gaba daya kasa.

Karin bayani