Babu kasar da ta fi Nigeria barayi —Magu

Shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nigeria zagon-kasa, Ibrahim Magu, ya shaida wa BBC cewa ba a taba yin irin sace-sacen da aka yi a matakin gwamnatin tarayyar kasar ba a duk fadin duniya.

Ibrahim Magu ya bayyana hakan ne a Kano bayan ya gudanar da wani taron manema labarai.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A cewarsa, "Idan ka ga sace-sacen da aka yi a matakin gwamnatin tarayyar Nigeria, batu ne da ba ma a magana saboda bacin sa.Ba a taba yin irin wannan ba a Nigeria da kusan ma duniya baki daya."

Shugaban na EFCC ya ce yanzu abin da hukumarsa ta mayar da hankali a kai shi ne ta kwato kudaden da aka sace kafin ta soma hukunta mutanen da ake zargi da sace su.

A baya bayan nan dai EFCC ta kama manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, da manyan jami'an jam'iyyar PDP bisa hannu a badakalar da ta shafi kudi.

Babban mutumin da EFCC ta kama shi ne Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa Jonathan shawara a kan sha'anin tsaro bisa zargin sace fiye da dala biliyan biyu da aka ware domin sayen makaman da za a yi yaki da Boko Haram da su.