Nassarawa: wata ta rasa aikinta saboda facebook

Image caption An kori Rukayya daga aiki saboda tayi kalamai a facebook

A Najeriya, wani sabon sabani ya sake shiga tsakanin gwamnatin jihar Nasarawa da kungiyar kwadagon jihar, mako biyu da sasanta rikicin da suka yi fama da shi na rashin biyan wasu hakkokin ma'aikata, lamarin da ya sa 'ya'yan kungiyar shiga yajin-aiki.

Yanzu dai Kungiyar kwadagon ta hassala ne sakamakon korar da aka yi wa wata diyarta daga aiki, mai suna Rukayya Tijjani Usman, wadda ke aiki a ma'aikatar shara'a, kuma ta ba wa gwamnati wa'adin mako biyu domin ta mai da ita bakin aiki.

Gwamnati dai ba ta fadi dalilin korar ba, amma wasu na zargin cewa tana da nasaba da wasu kalaman da ta wallafa a shafinta na facebook, wadanda ba su yi wa gwamnati dadi ba.

To ganin cewa ba kasafai ake barin ma'aikata na magana a kan gwamnati ba,to ko me ya kai Rukayya Tijjani Usman wallafa irin wadannan kalamai nata a shafin facebook?

Ga dai abin da Rukayya ke cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti