'Yan Saudiyya na neman 'yanci

Image caption 'Yan Saudiyya na neman yanci ta kafafen sada zumunta na zamani

A duk lokacin da ake batun 'yanci, kungiyoyin kare hakkin dan adam za su shaida maka cewa Saudiyya tana cikin kasashen da basa kare hakkin dan adam. Sai dai mai yiwuwa idan aka kwatanta da sauran kasashe za iya cewa babu cikakken 'yanci a kasar Saudiya, don haka 'yan kasar na yin amfani da shafukan sada zumunta domin yi wa gwamnati bore.

A wannan shiri na musamman na BBC mai taken "'Yan Saudiya a kafofin sadarwa na zamani," za mu bayar da labaran wasu masu shafukan twitter wadanda suka yi badda kama, wadanda dukkansu suke rajin neman 'yanci a Saudiyya.

Amma wanne tasiri wannan boyayyiyar rayuwa ke da shi kan masu yin ta?

Hussein ya shaida mana yadda rayuwa take ga tsirarin mabiya shi'a a kasar.

"Youssef" dan shekara 20 ya bayar da labarin yadda 'yan daudu ke rayuwa a Saudiyya.

Shi kuwa Mazen wanda ya rasa idanunsa a lokacin da yake dan shekara 7, ya bayar da labarin yadda kafofin sadarwa na zamani suka taimaka wajen sauya duniyarsa da kuma bashi 'yanci na sabon imani a matsayinsa na makaho.

MAZEN
Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Mafi yawan masu matasa a yanzu kan yi amfani da shafin Twitter don bayyana ra'ayinsu

Na rasa idanuna ina da shekara bakwai a duniya.

Amma sai duniyata ta sauya a lokacin da na gano wasu kayan aiki na intanet da aka yi domin makafi.

A lokacin ne na gano wata majalisa ta Larabawa wadanda basu yarda da samuwar Ubangiji ba.

Na kadu matuka, ban taba sanin akwai mutanen da suka bar Musulunci ba.

Na yi kokarin na ganar da su gaskiya cewa suna kan hanyar bata ne.

Amma a lokacin ne komai ya fara sauyawa, imanina ya fara rawa.

Yanzu haka shekara hudu kenan da na bar Musulunci.

Sai na bude wani shafin Twitter na yi badda kama domin na samu hanyar bayyana ra'ayina a fili.

A bayyane, barazanar da na gani daga wajen al'umma ta fi ta hukumomi ma.

Babban abin da ya fi damuna shi ne ka da iyayena su gani don kuwa za su sallamani ne.

Ba a dade ba kuwa matata ta ji ina wata hira da wasu, anan ta san me nake ciki.

A yanzu haka dai mun raba daki da ita, maganar gaskiya ita ce ba ma tare.

Ina da da daya amma bai sani ba tukunna.

Idan da a ce zan iya bayyana masa abinda na yi imani da shi, to da zan ce masa addini ba gaskiya ba ne, kagaggen abu ne da mutane suka kirkiro, amma kuma ba zan iya hakan ba.

Zan bar shi kawai ya gano abinda ya yi imani da shi da kansa.

HUSSEIN
Image caption Ana yawan samun rikici tsakanin mabiya Sunna da na Shi'a a Saudiyya

An haife ni na kuma girma a garin al-Qatif

Nan ne garin da 'yan shi'a suka fi yawa a Saudiyya.

Shekaru kadan da suka gabata, wani abokina mabiyin Sunna ya rokeni in shaidawa kotu mazhabar da yake bi.

Sai magatakardan kotun ya ce ba za a karbi shaidata ba saboda ni dan shi'a ne.

Ya ce ni ba Musulmi ba ne.

Akwai abubuwa da suka sha faruwa irin wadannan.

akwai wata rana muna cikin wata motar bas tare da sauran 'yan uwa mabiya shi'a muna dawowa daga al Qatif, sai aka kawo mana hari.

Sai mutane suka fara jifanmu da duwatsu a watar tashar samar da iskar gas a wani waje na zallar mabiya Sunna.

A lokacin da aka yi ta samun juyin-juya hali a wasu kasashen Larabawa a shekarar 2011, Saudiyya ma ba a bar ta a baya ba, amma mutane da dama ba su san hakan ta faru ba.

Kafafen yada Labarai sun yi shiru kamar ba sa nan.

Sai na ji ya kamata a ce wadannan labaran an watsa su an ji su a ko ina.

Don haka sai na bude shafin Twitter da wasu masu fafutukar iri na.

Hukumar bincike ta Saudiya ta samu damar gano wasu daga cikin mambobinmu.

An kama su an kuma yanke musu hukunci mai tsauri.

Kasata ba kasa ce ta kowa da kowa ba.

YOUSSEF
Image caption Masarautar Saudiyya na sa ido sosai kan masu kaucewa tsarin shari'ar Musulunci tare da hukunta su

Ni namiji ne amma ina daukar kaina a matsayin mace.

Na rubuta labaran kungiyar 'yan luwadi da madigo ta Saudiyya a shafin Twitter, don mutane su san da zamanmu.

A lokacin da nake matashi, na fada cikin soyayyar daya daga cikin 'yan mazan makarantar.

Na gaya masa irin son da nake masa sai muka fara soyayya, wadda ita ce alakata ta farko da wani.

A karon farko a rayuwata sai na ji ashe na cancanci a so ni.

Amma kowanne abu mai dadi dole ne yana da karshe. Sai na gano ashe shi bai taba sona ba.

Sai ya nadi hirarmu da shi ya aikawa sauran 'yan mazan ajinmu.

A lokacin da nake da shekara 18, na sanar da mahaifiyata.

Sai ta kai ni wajen likita.

A wannan lokaci ne na yi kokarin kashe kaina.

Na ji matukar takaici da na fahimci cewa na bata kunya ta kuma shiga halin bakin ciki.

Amma dai lamarin bai gama dagulewa gaba daya ba.

A lokacin da kanina ya gano halin da nake ciki, sai ya tambaye ni wanne irin saurayi ne ya rudi zuciyata haka.....

Sai na ce masa Zayn Malik ne. Sai ya ce "Ko da ni ne ma ba zan ki kwanciya da Zayn Malik ba."

Shekarata 20 a yanzu, kuma na san bana tare da kadaici.