Tusk zai gana da Erdogan kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'Yan gudun hijira

Shugaban majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk, zai gana da shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, don tattaunawa kan 'yan gudun hijira.

Shugabannin biyu, wadanda za su gana da misalin karfe daya na rana a agogon GMT, za su sabunta kudirinsu na tunkarar matsalar ta 'yan gudun hijira.

Dubban 'yan gudun hijira ne ke ci gaba da isa tsibiran da ke kasar Girka a kowacce rana bayan sun bar gabar tekun kasar Turkiyya.

Da dama daga cikinsu sun make a kasar ta Girka saboda shingayen da aka sa a kamn iyakokin kasar ta Turkiyya.

Kungiyoyin da ke bayar da agaji sun ce a halin da ake ciki akwai 'yan gudun hijira sama da 11,000 da aka tsugunar a sansanin Idomeni da ke kan iyakar Girka da Macedonia.