'Yan takarar shugabancin Amurka sun yi muhawara mai zafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Trump ya sha alwashin korar Musulmai daga Amurka.

An yi ta musayar kalamai masu zafi a muhawara ta baya-baya nan ta gidan talbijin tsakanin mutanen da ke son yin takarar shugabancin Amurka su hudu na jam'iyyar Republican.

Sukar da ake yi wa dan kasuwan nan Donald Trump mutanen da ke sahun gaba, ita ta mamaye muhawarar tsakanin sa da sauran abokan takarar sa.

Sanata Marco Rubio ya sanya alamar tambayar a kan ko masu kada kuri'a za su iya amince wa da kalaman da Mr Trump ke yi, musamman inda ya ce zai kori Musulmai daga kasar.

A nasa bangaren, Mr Trump ya zargi Mr Rubio da kunyata wadanda suka zabe shi, saboda rashin tabuka wani abun azo a gani a Majalisar dattawa.

Shi kuwa Sanata Ted Cruz ya bayyana shakku ne game da irin goyon bayan da Mr Trump ya bayar ga 'yan takarar shugabancin kasar a baya a karkashin inuwar jam'iyyar, yayin da dan takara na hudu kuma gwamnan jihar Ohio, ya mayar da hankali a kan batun daya shafi kasafin kudi da tattalin arziki.

Wannan dai wata rana ce da Donald Trump ya fuskanci sukar da ba'a saba ganin irinta ba tsakanin 'yan takarar jam'iyyar Republican.