Bai kamata mu sake yin kuskure ba - Kompany

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany, ya ce bai kamata kungiyar ta sake shan kashi ba idan har tana so ta dauki kofin gasar Premier na bana.

Liverpool dai ta doke City da ci 3-0 loss ranar Laraba - kuma shi ne karo na uku da suka sha kashi a jere.

Kungiyar ta City tana bayan kungiyar da ke kan gaba a tebirin gasar ta Premier, Leicester City, da maki 10.

Su ma kungiyoyin da ke gogayya wajen daukar kofin, Arsenal da Tottenham ba su yi nasara ba a wasan da suka yi.

Kompany ya ce: "Bai kamata mu sake yin kura-kurai ba."

Aston Villa za ta kai wa City ziyara har gida a wasan da za su yi a karshen mako, yayin da Leicester za ta bakunci Watford sannan Arsenal ta fafata da Tottenham.

Kompany ya kara da cewa, "Komai a rikice yake a kakar wasa ta ban. Babu wanda zai iya yin hasashen abin da zai faru.".