An ceto 'yan makarantar da aka sace a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce ba a biya ko kwabo ba ga wadanda suka sace 'yan matan.

An samu nasarar ceto 'yan matan nan uku 'yan makaranta da aka sace a Ikorodu ta jihar Lagos.

A hirar ta da yi da BBC, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta ce ba a biya diyya ba kafin a sako 'yan matan.

Rundunar ba ta yi bayanin ko an yi musayar wuta da wadanda suka sace 'yan matan ba kafin a sako su ba, ko kuma an samu nasarar chafke su.