Nigeria: Majalisa ta bara kan kudin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Ana saran a wannan watan ne 'yan Majalisar dokokin za su zartar da kasafin kudin 2016.

A Nigeria, wa su 'yan Majalisar dattawan kasar sun bayyana rashin jin dadin su game da kason da gwamnatin kasar ta ware a kasafin kudin 2016 ga wasu hukumomi don kula da 'yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar.

'Yan Majalisar sun bayyana cewa gwamnati ta ware naira biliyan daya da miliyan dari uku ga hukumar bada agajin gaggawa ta kasar wato NEMA yayin da kuma aka ware biliyan biyu da miliyan dari hudu ga hukumar kula da 'yan gudun hijira, lamarin da 'yan Majalisar suka ce ya yi kadan.

Shugaban kwamitin ayyuka na musamman a Majalisar dattawan wanda ke kula da 'yan gudun hijira Sanata Abdul Aziz Murtala Nyako ya shaida wa BBC cewa akwai kimanin mutane miliyan goma da rikicin Boko Haram ya rutsa da su a yankin arewa maso gabashin kasar.

A watan daya gabata ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alawashin daukar tsattsauran matakin ladabtarwa kan duk masu hannu a sassauya alkaluman kasafin kudin kasar na shekarar 2016, inda ya ce sauye-sauyen da aka yi ta bayan fage su ne suka sa kasafin kudin ya bambanta da wanda ya gabatar wa majalisar dokokin kasar.

Ana saran a wannan watan ne 'yan Majalisar dokokin za su zartar da kasafin kudin da shugaban kasar ya gabatar musu.