Hassan al-Turabi ya rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hassan al-Turabi, daya daga cikin manyan 'yan siyasar kasar Sudan, ya rasu, bayan ya yi shekaru 84 a duniya.

Hassan al-Turabi shine ya bullo da tsare-tsaren kafa gwamnati akan turbar Islama a kasar.

An kwashe shekaru da dama ana ganinshi a matsayin babban jigon kafa mulkin Shugaba Omar al-Bashir.

Bayan da ya bata da Shugaban Bashir ne a shekarar 1999 ya kafa jam'iyyar adawa. Mafi yawa daga cikin shekarun goman da suka biyo baya ya yi sune a gidan yari.

Hassan al Turabi na da zurfin ilmi sosai kuma masanin addinin Islama ne mai fada-a-ji a ciki da wajen Sudan.