An rufe gidan jaridar Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a Turkiyya sun yi wa ofishin gidan jarida mafi girma a kasar kawanya, bayan da hukumomi su ka kwace ta a ranar Juma'a.

'Yan sanda dauke da makamai na gadin kofar gidan jaridar, mai suna Zaman, wasu kuma na ciki sun tattare ko-ina.

A ranar Juma'a da daddare 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da bututun fesa ruwa, suka tarwatsa masu zanga-zanga, suka kutsa cikin gidan jaridar.

A dab'in da ta buga na karshe kafin mamaye tan, jaridar wannan lokaci ne mafi muni ga 'yancin aikin jarida a tarihin Turkiyya.

Jaridar Zaman dai na adawa sosai da Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Amurka da Tarayyar Turai sun soki kwace gidan jaridar da gwamnatin ta yi.