Trump da Mrs Clinton sun fadi a wasu jihohi

Image caption Mrs Clinton da Trump sun fadi a wasu jihohi

Wasu 'yan takarar shugabancin Amurka su biyu da ke gaba-gaba a zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican, sun samu nasara a jihohi biyu-biyu kowanne su.

Sanata Ted Cruz ya samu nasara a jihohin Kansas da Main, yayin da Donald Trump ya yi nasara a jihohin Louisiana, da Kentucky.

A wani taron manema labaru, Mr Trump ya yi kira ga abokin takarar sa Sanata Marco Rubio da ya janye daga takarar.

Senata Cruz dai ya yi ikirarin cewa shi ne ya fi cancanta fiye da Donald Trump wanda wasu fitattu a jam'iyyar Republican ke adawa da takarar sa.

A zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat kuwa, Sanata Bernie Sanders, ya do ke Hillary Clinton a jihar Kansas, kuma hasashe ya nuna cewa shi ne ya lashe zaben a jihar Nebraska.

An kuma yi hasashen cewa Mrs Clinton ita ce za ta lashen zaben a jihar Louisiana.