Ranar yaki da bauta a kasar Mauritania

Ranar yaki da bauta a kasar Mauritania Hakkin mallakar hoto
Image caption Ranar yaki da bauta a kasar Mauritania

A karon farko kasar Mauritania ta gudanar da ranar yaki da bauta.

Sama da shekaru talatin da suka gabata ne Mauritania ta haramta bauta a cikin kasar sai dai har yanzu matsalar ba ta sauya zani ba.

A bara Majalisar dokokin kasar ta zartar da dokar da ta bayyanna bauta a matsayin babban laifi, kuma ta kara shekaru ashirin a cikin hukuncin da za a yanke wa duk wani da aka samu da laifi .

A ziyarar da ya kai kasar ranar Juma'a Sakatare janarar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon ya yi kira ga gwamnati akan ta tabbatar ta aiwatar da dokar.

Masu fafituka suna zargin gwamnatin da amfani da fatar baka wajen shawo kan matsalar.