An hallaka jami'in APC a Rivers

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan bindiga sun kashe wani jami'in jam'iyyar APC a jihar Rivers, Mista Frankiline Obi, da matarsa da kuma dansa.

Mista Obi, wanda shugaban jam'iyyar APC ne na unguwa (Ward 4) a garin Omoku, an kashe shi ne lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a gidansa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Ahmed Kidaya Mohammed, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan bingidar sun harbe shi ne kafin su yanke kansa su tafi dashi.

Ya kuma ce sun harbe matar Mista Obin har lahira da kuma dansa, wanda shi ma yanzu ya mutu a asibiti a sababin harbin.

DSP Mohammed ya ce 'yan sanda na bincike sosai domin gano 'yan bindigar.

Ga cewarsa, kwamishinan 'yan sanda a jihar Musa Kimo ya ziyarci garin, inda ya yi wa iyalan mamatan ta'aziyya, ya kuma tura karin 'yan sanda a wajen.

Ya ce rundunar 'yan sanda ba ta sani ba ko kisan na da alaka da siyasa ko kuwa a'a.

Jihar Rivers dai na fama da ringimar siyasa tsakanin jam'iyyar PDP, mai mulkin jihar, da APC, mai adawa da ita a jihar amma ta na rike da gwamnatin tarayyar kasar.