An kai harin makamin roka kasuwar Aleppo

'Yan tawayen Syria
Image caption Shekaru biyar kenan da fara yakin Syria.

Kafar yada labaran Syria ta ce akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu a lokacin da aka harba wani makamin roka wata kasuwa da ke arewacin Aleppo.

Sai dai wasu rahotannin sun ce wadanda suka rasu ba su kai yawan hakan ba, inda suka ce mutane uku ne kadai suka mutu a harin.

Mako guda kenan da al'umar kasar ke cikin jin dadin tsagaita wutar da bangarorin da ke rikici da juna suka yi.

Ita ma hukumar da ke sa ido kan take hakkin bil'adama a Syria ta ce ranar lahadi ta kasance rana ma fi walwala da jin dadi ga al'umar kasar tun fara aikin yarjejeniyar.

A shekarar 2011 ne kasar Syria ta fada rikicin da ya bukacin shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga mukaminsa, inda daga bisani ya koma yakin basasa.

Akalla mutane 250,000 ne suka mutu tun fara rikicin, ya yin da sama da miliyan 13 suka bar muhallansu.