Tomlinson da ya kirkiri Email ya rasu

Tomlinson ne ya fara aikewa da sakon Internet Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Ba kuma zai tuna abinda wasikar sa ta farko ta kun sa ba.

Ba'amurken nan da ya kirkiro hanyar tura wasika ta intanet, wato Ray Tomlinson ya rasu, yana da shekara 74 a duniya.

A shekarar 1971 ne ya fitar da basirar tura wasika ko sakonni ta hanyar laturoni ko intanet daga wani mutum zuwa wani, kuma a wannan lokacin ne wasikar email ta farko, lokacin da yake aiki a Boston, a matsayin Injiniyan komfuta.

Kazalika shi ne ya fara amfani da wasalin @ mai lankwasa wajen tsara adireshin wasikar intanet, har ta kai ga ya zama babbar siffa a cikin adireshin email.

Mr Tomlinson dai ya ce ba zai iya tunawa da abin da wasikarsa ta farko da ya fara turawa ta intanet ta kunsa ba.