Taron kan tattalin arzikin Najeriya

Image caption Za a gudanar da taron tattalin arzikin Najeriyar ne a ranakun 7 da 8 ga watan Maris.

An bude wani taron koli na kwanaki biyu domin duba halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga ranar Litinin.

Taron wanda ke gudana a babban birnin kasuwanci na kasar wato Legas, zai duba yadda duniya ke kallon tattalin arzikin Najeriya, da kuma hanyoyin zuba jari a kasar da ma yankin yammacin Afrika.

Mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo da hamshakin dan kasuwar na Aliko Dangote na daga cikin manyan mutanen da za su halarci taron.

Sauran bakin da ake sa ran za su halarci taron sun hada da gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da na jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura da kuma jihar Anambra, Willie Obiano.

Wannan taro dai shi ne na goma sha daya cikin irinsa da jaridar Economist ke shiryawa a Najeriya, kuma shugaban kanfanin jaridar ne zai jagoranci taron.